Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

‘Yan tawayen Syria sun zargi Amurka da yin zagon kasa

‘Yan Tawayen kasar Syria, sun zargi kasar Amurka da zagon kasa, a kokarin da suke na kifar da gwamnatin shugaba Bashar al Assad, a wani yanayin da ke tabattar da baraka tsakanin ‘Yan Tawayen da Amurka.

Wasu daga cikin  'Yan tawayen kasar Syria masu yaki da Gwamnatin Shugaban kasa Bashar Assad
Wasu daga cikin 'Yan tawayen kasar Syria masu yaki da Gwamnatin Shugaban kasa Bashar Assad REUTERS/Zain Karam
Talla

Kwanaki biyu kafin gagarumin taron da za’a gudanar na shugabanin ‘Yan adawar kasar Syria a Qatar, hadaddiyar kungiyar ‘Yan Tawayen kasar, ta zargi kasar Amurka, kan sukar da ta yi cewar, ba ta wakiltan daukacin ‘Yan kasar ta Syria.

Sanarwar da kungiyar ta bayar, sun ce duk wani shirin tattaunawa wajen mayar ga ragamar tafi da kungiyar ga wasu mutane dabam, ko kuma kafa wata kungiyar, zai zama zagon kasa ga yakin da suke yi na kifar da shugabancin shugaba Bashar al Assad.

Kungiyar tace, duk wani yunkuri na sake fasalin ta, zai zama nasara ce ga shugaba Bashar al Assad, yayin da ta tabbatar da karbar taimakon sama da Dala miliyan 40 daga kasashen duniya.

A baya Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta bayyana kungiyar ‘Yan Tawayen a matsayin wadanda ba su wakilatar daukacin ‘Yan Tawayen kasar, inda ta bukaci a yi wa kungiyar garambawul, don ganin ta kunshi wadanda ke yaki da dakarun gwamnati a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.