Isa ga babban shafi
Saudiya

Aikin Hajji, taron Mutane mafi girma a Duniya

A yau Laraba ne, 24 ga watan Oktoba a ke fara aikin Hajji a Birnin Makka kasar Saudi Arebiya. Kimanin Musulmi Miliyan Hudu daga kasashe 180 ke gudanar da aikin Hajjin Bana wanda shi ne taron Mutane mafi girma a Duniya duk shekara.

Mahajjata da ke aikin Hajji a kasar Saudiya a bana.
Mahajjata da ke aikin Hajji a kasar Saudiya a bana. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

A bana ana gudanar da aikin Hajjin ne cikin tsauraran matakai saboda tashin hankalin da ake ci gaba da samu a kasashen Yankin Asiya.

Aikin Hajji yana cikin Shika Shikan Musulunci guda Biyar da aka wajabta wa Musulmi ya gudanar akalla sau daya a rayuwar shi idan har yana da wadata kuma yana cikin koshin lafiya.

A bana Mahajjata Mata daga Najeriya da Nijar sun fuskanci barazana daga mahukuntan Saudiya game da batun Muharrami. Wasunsu da dama an dawo da su gida saboda wannan matsalar.

Akwai kuma tsauraran matakai da Saudiya ta dauka wajen bayar da izinin shiga kasar ga Mahajjatan kasar Iran. Matakan kuma sun hada da haramtawa Mahajjatan Iran gudanar da Fatawa a sansanin masu aikin Hajji.

Ministan Cikin Gidan Saudiya Yarima Ahmad ya yi gargadin daukar mataki ga duk wanda ya karya dokokin gasar Saudiya.

Mahajjatan kasar Syria kuma da ke gudun Hijira a kasashen Jordan da Turkiya da Lebanon sun samu kulawa ta musamman daga mahukuntan Saudiya.

A bara dai Mahajjata sama da Miliyan Uku ne suka aiwatar da aikin Hajji amma a bana Mahajjatan za su haura Miliyan Hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.