Isa ga babban shafi
Syria-China

Kasashen Yammaci ne matsalar rikicin Syria, inji China

Wata babbar Jaridar kasar China mai magana da yawun gwamnati ta zargi kasashen Yammaci wajen dakile hanyoyin sasanta rikicin Syria, a dai dai lokacin da wani babban jami’in kasar Syria ke ziyara a Beijing domin tattaunawa da shugabanin China.

Hotun Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad yana cin wuta
Hotun Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad yana cin wuta Bulent Kilic/AFP
Talla

Jaridar People's Daily da ke Magana da yawun gwamnati, tace kasar China za ta yi kokarin fito da hanyoyin kawo karshen rikicin Siyasar kasar Syria a tattaunawar da shugabannin kasar za su yi da wani mai bai shugaba Bashar Assad shawara.

Kasar China da Rasha sun dade suna hawa kujerar na-ki a zauren kwamitin tsaro game da amincewa da kudirin magance rikicin Syria inda kasashen biyu ked a sabanin ra’ayi tsakaninsu da Amurka da Birtaniya da Faransa wadanda suka taka rawa wajen kawar da Kanal Gaddafi na Libya.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 23,000 suka mutu tun fara zanga zangar adawa da gwamnatin Bashar Assad a watan Maris din bara. Rahoton Majalisar yace sama da mutane 14,000 suka yi gudun hijira zuwa wasu kasashe daga Syria.

Tsohon Firaministan Syria Riad Hijab wanda shi ne jami’in gwamnatin kasar mafi girma da ya canza sheka zuwa bangaren ‘Yan adawa yace gwamantin kasar na kan rugujewa.

Riad yace yanzu kashi 30 cikin 100 na kasar ne kawai ke hannun gwamnatin, yana mai cewa gwamnatin Assad ba ta da Karfin soja ko na tattalin arziki.

Tsohon Firaministan wanda ya tsere zuwa Jordan a makon jiya, ya yi wannan jawabin ne a dai dai lokacin da kungiyar kasashen Musulmi ta OIC ke tunanin dakakatar da wakilcin kasar Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.