Isa ga babban shafi
Kasar Jamus

An kulla yarjejeniyar hadin kai tsaknin Jamus da Indonesia

Shugabar Kasar Jamus, Angela Merkel, ta saka hanu a wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin kasarta da kasar Indonesia. 

Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel
Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel REUTERS
Talla

Merkel ta saka hanun ne a wata ziyara da ta kai wa shugaban kasar ta Indonesia a karon farko, Susilo Bambang, ta na mai cewa yarjejeniyar za ta kara habaka harkar kasuwanci a tsaknin kasashen biyu.

Haka kuma yarjejeniyar kamar yadda Kamfanin Dillancin labaran Faransa ya fada, za ta karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu ta fuskokin, tsaro da tattalin arziki da cigaba da kiwon lafiya da sauransu.

A yau ne a cikin ziyarar ta Merkel, a ke sa ran za ta ziyarci cibiyar da aka samar don sanar da jama’a yiwuwar aukuwar guguwar tsunami a kasar ta Indonesia.

A cewar ta, kasashen biyu za su karu musamman ta fuskar cibiyar da aka samar ta sanar da yiwuwar guguwar tsunami wacce ta jaddada cewa ya na daga cikin misalai da kasashen za su mai da hankali a kai.

Harkokin hadahadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu a shekarar bara ya kai har kudin Euro 3.4 biliyan kamar yadda alkaluma su ka nuna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.