Isa ga babban shafi
Sharhin Jaridu

Sharhin jaridun Fransa da Afrika

Jaridar Liberation ta kasar Fransa ta mako hoton shugaban kasar Nicolas Sarkozy dan takarar jam’iyar UMP na cewa, babu yadda za’a yi jam’iyarsa ta nemi hadin guiwa da yar takarar da ta zo uku a zagaye na farko na zaben da aka yi ranar lahadi, uwar gida Marine Le Pen, wace ya danganta da zama marar kirki, tare da cewa, ko da magoya bayanta sun kada masa kuri’a a zagaye na 2 na zaben da za a gudanar ranar 6 ga watan mayun gobe, ko da kuwa ya lashe zaben ba zai ba jam’iyarta ta Front national (FN), ta yan mazan jiya mukamin minista ba. Jaridar Le Figaro cewa ta yi, yanzu haka dai Francois Holland dan takarar jam’iyar Socialite ya shawo kan magoya bayan jam’iyar ta yan kishin kasa ta Marine Le Pen, kalmar da ke nuna cewa, tarihin kasar Fransa na kan hanyar karkata bangaren yan adawa. An shiga yakin iskar Gaz tsakanin Masar da Isra’ila. jaridar Le Figaro ta ce kasar Masar ta yanke shawarar barin baiwa Izra’ila makamashin Gaz, kamar yadda kamfanin samar da Gaz na kasar ta Masar Egas ya sanar, sakamakon abinda kin biyan kudaden da Izra’ilar ta yi na tsawon watanni 4. A jiya talata ne Béatrice Stockly yar kasar Suisse ta isa a birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso, bayan da aka sace ta a garin Tumbuctu, garin da ta ki ta ficewa daga cikinsa lokacin da ya fada ga hannu yan tawayen kungiyar Ansar Din. Jaridu sun yaba da wannan saki da aka yi matar, jaridar L’Observateur ta Burkina Faso cewa ta yi Béatrice Stockly, ta yi sa’ar gaske, a yayin da wasu turawan da aka yi garkuwa da su ke ci gaba da kasancewa ga hannu yan al’kaida a yankin Sahel, ita kuma kwanaki 10 kawai ta yi a hannun wadanda suka sace ta aka kubutar da ita.Ita kuma jaridar Liberte ta kasar Togo yaba wa yan Kasar Burkina faso ta yi kan wannan kokari da aka yi wajen kubutar da matar. Jaridar ta ce shekaru da dama da suka gabata shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaoure, ke taka muhimmiyar rawa wajen ganin an sako mutanen da ake garkuwa da su a yankin Sahel.Sabin mahukumtan kasar Mali na jan Kafa wajen bayyana mambobin gwamnatin, sama da mako guda bayan da aka nada Frayi Ministan rikon kwaryar kasar.tuni dai kafofin yada labarai sun shiga tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan tsaiko. Jaridar Le Pays ta Burkina Faso cewa ta yi, ya dace a yi taka tsantsan domin kar wannan tsaiko ya jawo rarrabuwar kanu tsakanin yan siyasar kasar, ma’ana tsakanin yan siyasar dake tare da sozojin da suka kifar da gwamnati, da kuma yan siyasar da ke kin jinin juyin mulkin na ranar 22 ga watan maris da ya gabata. 

Quelques unes de médias anglophones titrant sur le scrutin d'hier, dans un kiosque à Nice le 23 avril 2012.
Quelques unes de médias anglophones titrant sur le scrutin d'hier, dans un kiosque à Nice le 23 avril 2012. REUTERS/Eric Gaillard
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.