Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Obama yace Amurka ba zata yi gaggawar Ficewa daga Afghanistan ba

Shugaban kasar Amurka Barack Obama yace dakarun kasarsa ba zasu yi gaggawar ficewa daga kasar Afghanistan ba, bayan sojan Amurka ya hallaka mutane 16. Obama ya ce tilas dakarun kasashen duniya su bi matakan da suka dace wajen janyewa daga Afganistan.

Dakarun Amurka a Afghanistan
Dakarun Amurka a Afghanistan REUTERS/Ahmad Nadeem
Talla

Sakataren tsaron kasar ta Amurka Leon Panetta ya fadi cewa sojan da ya yi harbin zai fuskanci hukunci kisa muddun aka same shi da laifi, Kuma kotun sojan Amurka ce zata yi shari’ar.

Kisan da ya faru a Birnin Kandahar ya sake gurgunta dangantakar da ke tsakanin Amurka da Afghanistan.

Da safiyar yau Talata daruruwan dalibai ne suka hada wani gangami a gabacin Jalalabad domin la’antar harin da Sojan Amurka ya kai tare da shewar la’antar Amurka da Obama.

Tuni dai kungiyar Taliban ta aiko da sakon daukar fansa domin mayar da martani ga kisan mutane 16 da kuma kona Al Qur’ani da dakarun Amurka suka yi a kwanan baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.