Isa ga babban shafi
China-EU

kasar China zata daina sayen jiragen saman kamfanin Airbus na turai

A wata fira da jaridar Wall Street ta yi da shi a yau litanin, jakadan kasar Sin a kungiyar tarayyar Turai ya bayyana cewa, kamfanonin jiragen saman kasarsa za su fi maida hankali wajen sayen jiragen saman kamfanin Boeing fiye da na Airbus, sakamakon harajin da kasashen turai suka aza kan fitar da gurbatacen hayaki mai guba.A ranar alhamis da ta gabata ne, Kamfanin kera jiragen saman Airbus na nahiyar Turai ya bayyana cewa, kasar Sin ta dakatar da kwangilar sayen jiragensa, a matsayin mayar da martani kan harajin da kasashen turan suka azawa dukkanin kamfanonin jiragen saman dake zirga-zirga a sararin samaniyar turai.A cikin wata wasikar hadin guiwa da kamfanin na Airbus tare da wasu kamfanoni jiragen saman turai guda shida suka fitar a yau litanin, sun nemi shuwagabanin gwamnatocin kasashen Jamus, Britaniya, Spain da Fransa, da su kaucewa yakin kasuwanci da wannan dokar haraji ta jawo a duniya. 

DR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.