Ranar Tunawa da gudumawar da mata suka bayar
A yau Ahamis takwas ga watan Maris shekara ta 2012, ya yi daidai da ranar bikin mata karo na 47 a duniya, inda mata da kungiyoyin mata suka shirya bukukuwan tunawa da ire iren ci gaban da mata suka samu.
Wallafawa ranar:
A jiya Laraba jajibirin ranar mata ta MDD, Shugaban kasar Algeriya Abdula’aziz Butaflika ya jinjinawa gudunmuwar da mata suka bayar a lokacin yakin 'yantar da kasar daga kasar Faransa, wanda kuma ya zo daidai da ranar da shekaru 50 da kasar ta tamun yancin kanta.
A cikin jawabin da ya gabatar Butaflika ya bayyana cewa, matan kasar ta Algeriya sun taka muhimmiyar rawa a lokacin yakin neman 'yancin kan, wanda yasa ba za a taba manta da su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu