Isa ga babban shafi
Syria-Tunisia

Taron kawayen Syria a Tunisia, Rasha da China sun kaurace

Wakilan kasashen Duniya sama da 60 ne zasu halarci taron kawayen Syria da za’a gudanar a kasar Tunisia domin tattauna hanyoyin da za’a kawo karshen rikicin Syria tare da matsin lamba ga Bashar Assad ya amince tallafi ya cim ma fararen hula a yankunan kasar.

hare haren da ake kai wa birnin Homs na kasar Syria
hare haren da ake kai wa birnin Homs na kasar Syria REUTERS/Handout
Talla

Akwai dai laguden wuta da hare hare da ake kai wa a birnin Homs, kuma ana tunanin taron kawancen kasashen zasu nemi hanyoyin inganta huldar Diflomasiya domin mara wa ‘Yan adawa baya.

Sai dai kasashen Rasha da China kawayen Bashar Assad zasu kauracewa zauren Taron wanda ya kunshi kungiyar kasashen Larabawa da Tarayyar Turai da Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton.

Rasha da China sun taka rawa wajen kawo cikas ga yunkurin kasashen Turai da Larabawa wajen hawa kujerar na-ki ga kudirin Majalisar Dinkin Duniya game da Syria.

Hillary Clinton ta shaidawa manema Labarai cewa zasu yi kokarin nemo hanyoyin kawo karshen mulkin Assad tare da samar da gwamnatin demokradiyya ta wuccin gadi.

Ministan harakokin wajen kasar Faransa Alain Juppe, yace taron wani mataki ne na gargadi ne ga Assad da magoya bayan shi.

‘Yan rajin kare hakkin Bil’adama sun ce sama da mutane 7,000 ne aka kashe tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar Al Assad a watan Mayun bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.