Isa ga babban shafi
MDD-Somalia

MDD ta yi na’am da kawancen bangarorin Somalia

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bukaci bangarorin siyasar Somalia, da su aiwatar da yarjejeniyar sabuwar Gwamnatin da aka amince da ita a karshen mako. Yarjejeniyar ta kunshi shugabanin Yankunan Puntland da Galmudug, da ke cin gashin kansu, da kuma kungiyar da ke yaki da Al Shabaab.

Ban Ki-moon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Ban Ki-moon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Talla

Yarjejeniyar da aka cim ma a birnin Garowe bagarorin sun amince a samar da tsarin Majalisa a kasar.

An dade ana kokarin sasanta bangarorin Somalia tsawon shekaru 20 domin kawo karshen rikicin kasar. Amma  har yanzu ana ci gaba da yaki da kungiyar Al Shabab da ta karbe ikon tsakiya da kudancin Somalia tare da yaki da gwamnatin Somalia da ke samun goyon bayan kungiyar Tarayyar Afrika.

Kakakin kungiyar Al shabeb Sheikh Ali Mohamud yace wannan kawancen babu wani abun da zai haifar wa Somalia illa cim ma muradun kasashen yammaci na mulkin Mallaka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.