Isa ga babban shafi
Amurka

Republican: Romney ya lashe zaben fitar da gwani a Florida

Mitt Romney dan takarar shugaban kasar Amurka karkashin Tutar Jam’iyyar Republican ya lashe zaben zaben fitar da gwani a Jahar Florida, da kashi 46 na kuri’un da aka kada inda ya doke abokin karawarsa Newt Gingrich wanda ya zo na biyu da kashi 32.

Mitt Romney,Dan takarar Jam'iyyar Republican lokacin yakin neman zabensa a Jahar Florida
Mitt Romney,Dan takarar Jam'iyyar Republican lokacin yakin neman zabensa a Jahar Florida REUTERS/Mike Carlson
Talla

Bayan wannan nasara, Romney ya gargadi shugaba Barack Obama, cewar an zabe shi ne domin yin shugabanci, amma ya koma mabiyi, saboda haka lokaci yayi da zasu kawar da shi.

Nasarorin da Mitt Romney ya samu a Jahohin Carolina da Florida shi bayyana matsayinsa wanda zai kasance babban mai hamayya da Barack Obama a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Nuwamba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.