Isa ga babban shafi
Indonesia

Ziyarar Obama a Indonisiya

A ziyararsa ta kwanaki goma yankin Asiya, Shugaba Obama a yau talata ya sauka kasar Indonisiya, a wani kawance da shugaban ke neman kullawa da kasar kan harakokin kasuwanci da ci gaban demokradiyya. A daidai wannan lokacin Obama na ziyartar kasar ne a matsayin ziyartar gida, bayan da shugaban ya kwashe shekaru hudu yana zaune a kasar lokacin da yana yaro.Ziyarar Obama zuwa kasar wacce tafi kowacce kasa yawan musulmi a duniya da kuma a yanzu haka ke cikin zullumi na bala’in da ya aukawa kasar na aman wutar dutsin Marapi a kwanan baya.Shugaban a yau, ya bayyana irin ci gaban da kasar ta samu na fita daga mulkin danniya zuwa mulkin demokradiyya, inda Amurka ta taimaka wajen bunkasa kungiyoyin fararen hula wajen yaki da keta hakkin Bil’adama da kuma cin hanci da karbar rashawa a kasar. A gobe ne dai ake sa ran shugaban zai kai ziyara manyan masallatan kasar da suka hada da masallcin Itiqlal, masallaci mafi girma a kudu maso gabacin Asiya  

Shugaba Obama da Shugaban kasar Indonisiya Susilo Bambang Yudhoyono a Jakarta
Shugaba Obama da Shugaban kasar Indonisiya Susilo Bambang Yudhoyono a Jakarta Photo: Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.