Isa ga babban shafi
Indonesia

Ana ci gaba da ceto Al'umma a Indonisiya

Ma'aikatan ceto da kungiyoyin agaji a kasar Indonesia na ci gaba da gudanar da aikin ceto na kokarin gano wadanda ke da sauran kwana bayan wasu bala'oi da suka afkawa sassa daban daban na kasar.Kauyukka da dama ne dai suka wanke, gidaje da dama kuma suka shafe sanadiyar wata mummunar girgizar kasa da ta auku a yammacin Sumatra sakamakon wani tarwatsin amon wuta da duwatsu suka fara yi a ranar litinin din da ta gabata.Jami’an kasar sun bayyana cewa a kalla mutane 154 ne suka rasa rayukansu kuma sama da mutane 400 ne suka salwanta sanadiyar aukuwar al’amarin.“Muna kokarin lalubu wadanda suka salwanta kuma kokarin da muke ke nan cikin gaggawa, muna tunanin wasunsu sun kutsa ne cikin duwatsun amma kuma wasunsu dole sun mutu”. Tabakin shugaban hukumar ceto ta kasar ke nan Harmensyah.Wani kauye da ke da nisan kilomita fiye da dari da tsakiyar tsibirin Java, an ruwaito cewa Mutane sama da 29 ne dai suka mutu bayan da manyan duwatsun kasar na Merapi suka fara fidda amon wuta a ranar Talata.Jami’an kasar dai a yanzu haka sun bayyana cewa mutane sama da dubu Ashirin da Tara ne suka nemi matsuguni a birnin Yogyakarta.Hukumomi kuma na ci gaba da kokarin kwashe dubban mutane a wasu kauyuka dake kusa da wurin da dutsen yayi aman wuta, kodayake suna fuskantar kalubale a yanzu haka. 

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.