Isa ga babban shafi
UN

Majalasar dumkin duniya Kira ga taimako

Babban jami’in hukumar jinkai na majalasar dumkin duniya mai barin gado ,John Holmes ya furuta cewa ,a wanan shekara ,hukumar na da bukatar milyar 9 da digo 5 na dallar Amurika ,domin taimakama mutane milyon 53 da ke da bukata a cikin kasashe 34 na duniya.A shekarar da ta gabata ,milyar 7 ne kawai hukumar ke da bukata domin wadatar da jama’a a cikin shekara ta 2010,aman kuma daga baya alkaluma su ka canza sabili da gilgizar kasa a kasar Haiti da kuma matsalar karamcin kalaci a cikin kasashen yankin sahel da kuma kasashen tsakiya Afrika.A halin yanzu dai ,kishi 48 cikin 100 na taimakon da ake bukata ya samu.Milyar 4 da digo 9 na dallar Amurika ne kawai ya rage a samu jimullar kudin da ake bukata.Matsalar kalaci da cutar tamowa sun yi kamari a kasar jumhuriyar Nijar da ta Cadi sabili da rashin ruwan sama wadataci da kuma cikama da ba ta nuna ba a gonakin manoma. 

Une vue générale de la réunion des ministres des Affaires Etrangères du Sahara à Alger, le 16 mars 2010.
Une vue générale de la réunion des ministres des Affaires Etrangères du Sahara à Alger, le 16 mars 2010. Reuters/Louafi Larbi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.