Isa ga babban shafi
Thailand

Gwamnati ta tsawaita dokar ta baci

Gwamnatin kasar Thailand ta tsawaita dokar ta baci da aka saka cikin yankuna 19 na kasar, da suka hada da Bangkok babban birni, saboda tsaron yuwuwar sake samun tashin hankali.An fitar da dokar ta bacin cikin yankuna biyar, bayan karewar wa’adin na watanni uku, sakamakon daidaituwar lamura.An kafa dokar yayin zanga zangar nuna kiyayya wa gwamnatin kasar farkon wannan shekara, abunda yayi sanadiyar hallaka mutane 90.PM Abhibot Vejjajiva ya ce za a kawar da dokar sannu a hankali.Bisa tsarin kasar ta Thailand, jami’an tsaro nada izinin cafke mutun na tsawon kwanaki 30, ba tare da caji gaban kotu ba, karkashin dokar ta baci.

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.