Isa ga babban shafi
Girka

China zata saka jari a Girka mai fama da karayar tattalin arziki

Kasar Sin wato China ta sha alwashin karfafa gwuiwar saka jari a kasar Girka da bashi ya yi wa kanta, har ma Chinan wadda ita ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Asia ta sanya hannu kan hadin-gwuiwa ta fuskar sufurin jiragen ruwa da Girkan.Baya ga wannan kuma, kasar ta Sin ta kulla yarjejeniyoyin kasuwanci har goma sha uku da Kamfanonin Girka.Mataimakin Firayi Ministan Sin Zhang Dejiang ya fada a yayin rattaba hannun cewa gwamnatin China zata karfafa gwuiwar ‘yan kasuwar Sin su je kasar ta Girka su zuba jari.Bayan ganawarsu da takwaransa na Girka, Zhang ya bayyana kudirin kasashen biyu na kyautata dangantaka a tsakaninsu, tare da yin aiki tare, don magance mummunan tasirin karayar tattalin arziki, da ya durkusar da Girkan.  

Shugaban kasar China Hu Jintao
Shugaban kasar China Hu Jintao Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.