Isa ga babban shafi
Thailand

Gwamnati ta yi watsi da neman tattaunawa da masu zanga zanga

Gwamnatin kasar Thailand ta yi watsi da neman tattauanwar da masu zanga zanga sanye da jajayen kaya su ka yi, bayan mutuwar akalla mutane 67 tare da jefa kasar cikin zaman tararrabi.Dakarun sojan kasar sun ci gaba da dillace yankin da masu zanga zanga nuna kiyayya ga gwamnatin kasar su ka mayar tunga.An hallaka fiye da mutane 60 yayin da wasu daruruwa su ka jikata, amma masu zanga zangar na ci gaba amfani da roban harbi da bam kirar hanu akan dakarun sojan dake harbi da harsasai na gaskiya.Akwai dubban masu zanga zangar a cikin sansanin duk da wa’adin da gwamnatin kasar ta Thailand ta diba, da su ka hada da mata da yara.Shugabannin masu zanga zangar sun amince da tattauanwa da gwamanti bisa shiga tsakani daga majalisar dattawa, kwanaki biyar bayan zanga zangar ta koma tashi hankali da dakarun kasar.

Rikicin kasar Thailand na kara baci
Rikicin kasar Thailand na kara baci
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.