Isa ga babban shafi
Philippines

Dangin tsohon Shugaba Aquino Na Nasara

Rahotanni daga kasar Philippine na nuna cewa Benigno Aquino, dan tsohon Shugaban kasar Corazon Aquino na shirin hawa kujeran Shugabancin kasar, bayan zaben da akayi ajiya.Manny Villar, daya daga cikin yan adawa ya janye daga takaran ganin cewa Benigno Aquino na neman lashe zaben.Shi dai Benigno ba shine kawai daga jinin gidan tsohon Shugaban kasar dake hankoron hawa babban mukami akasar ba, domin  Uwargidan tsohon Shugaban kasar Imelda Marcos mai shekaru  80, na shirin lashe majalisar Wakilan kasar.'Danta Ferdinand Jr mai shekaru 52, zai kasance dan majalisar Dattijai, yayinda babbar 'yar tasu Imee mai shekaru  56 zata kasance Gwamna ayankin Ilocos Norte.Nasaran da dangin tsohon Shugaba Marcos suka samu na nuna cewa yanzu sun koma gadon mulkin kasar, bayan sun tsere zuwa Hawaii cikin 1986 sakamakon kazamin bore da akayi har Corazon Aquino ta har mulkin.  

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.