Isa ga babban shafi
Thailand

Masu Bore Sun Cigaba

Masu boren gamagari a kasar Thailand sun ja daga a wuraren da sukayi kakagida abirnin Bangkok yau, suna fadin cewa ala tilas sai Prime Ministan kasar ya sa ranar rusa majalisa da ranar da zaayi sabon zabe kafin su daina boren da suka kwashe watanni biyu suna yi.Masu boren, cikin jajjayen riguna sun nemi a gudanar da zabe cikin gaggawa inda suke nuna sun amince da zaayi sulhu kamar yadda Prime Minista Abhisit Vejjajiva ya nema, amma kuma suna bukatar takamaiman rana don zabe.Masu boren sunyi kanekane a harabar shagunan mutane, inda suka hana masu shagunan budewa, alamarin da yasa tafka asaran gaske.Tun ranar 7 ga watan jiya ne dai aka bayyana dokan ta baci, inda Soja da ‘yan sanda cikin shiri, dauke da makamai, ke ta sintiri dasa idanu a muhimman wurare. 

REUTERS/Sukree Sukplang
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.