Isa ga babban shafi
Thailand

Masu Bore Na Shirin Tsagaitawa

Masu bore don nuna kyamar Gwamnatin kasar Thailand sun amince dasu jingine, domin ayi sulhu gudun kada a sake samun zubar da jini.Yawan mutane 27 ne suka mutu sakamakon wannan bore na gama gari da akeyi akasar.Masu bore cikin jajjayen riguna sunce ba zasu gudanar da bore  cikin tsakiyar babban birnin kasar ba, sai dai kuma sun nemi Prime Ministan kasar Abhisit Vejjajiva daya fadi lokacin da zai rusa majalisar kasar domin a gudanar da sabon zabe, kuma ya janye dakarun daya jibge.Jagoran masu boren Veera Musikapong ya fadawa dafifin taron jamaa cewa sun karbi wannan shawara domin kauce kara zubar da jini akasar.Wannan bore wadda aka shiga mako na takwas anayi, ya kunshi marasa karfi ne da kuma maaikata, alamarin daya durkusar da harkokin yau da kullum abirnin Bangkok 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.