Isa ga babban shafi
Girka

Ministocin Kudade Na Turai Na Taro Gameda Halin Kudi Na Kasar Girka.

Ministocin Kudade na kasashen dake amfani da kudin Euro su 16, zasu halarci wani taron gaggawa a Brussels domin muhawara gameda batun komadan tattalin arzikin kasar Girka.   Prime Ministan Luxembourg Jean-Claude Junker ne ya bada sanarwan haka ayau.Junker wanda shine ke jagorancin Kungiyar Ministocin na Turai, kamar yadda mai magana da yawun sa ke cewa ya gayyato Ministocin Kudaden kasashen ne domin duba kudaden da zaa baiwa Girka rance.Wadannan kudade dai sun kai kudin Turai Euro biliyan 45 awannan shekaran wanda na hadin guiwa ne daga Asusun bada lamuni na duniya.Tunda fari Ministan Kudade na kasar Girka, George Papaconstantinou, ya fadi cewa dukkan wadanda ya dace su albarkaci wannan rance suna gabda zarta da rancen.  

Le Premier ministre luxembourgeois, Jean-Claude Juncker.
Le Premier ministre luxembourgeois, Jean-Claude Juncker. rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.