Isa ga babban shafi
Thailand

Soja Daya ya Hallaka yayin da wasu mutane 18 suka Jikata

A ci gaba da artabu tsakanin jami’an tsaron kasar Thailand da masu zanga zanga a Bangkok babban birnin kasar, yau Laraba soja daya ya hallaka yayin da wasu mutane 18 suka jikata. Masu kula da aiyukan agaji gaggawa sun tabbatar da faruwar lamarin na yau Laraba.Gwamnatin kasar ta tura daruruwan sojoji da Yan sanda domin toshe masu zanga zangar da su ka kawo cikas wa harkokin yau da kullum cikin tsakiyar birnin na Bangkok.Masu zanga zangar sanye da jajayen kaya su na bukatar Prime Minista (PM) Abhisit Vejjajiva ya rusa majalisar dokokin kasar tare da kiran sabon zabe, abun da ya yi watsi da shi, yanzu mutanen sun shafe makonni akan titunan babban birnin kasar.A yau Laraban kotun kula da tsarin mulkin kasar ta Thailand ta amince da bukatar hukumar zabe, na ta duba rushe jam’iyyar PM Vejjajiva, ta Democrat Party DP, saboda amfani da kudade ta janyoyin da su ka saba ka’ida.

© Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.