Isa ga babban shafi
Ukraine

Yan Majalisar Ukraine Sun Dambace

A kasar Ukraine, dazun nan Yan Majalisar Kasar suka dambace , yayin da suke tafka muhawara gameda batun ko ya dace su amince Sojan Ruwan kasar Russia su kafa sansaninsu akasar.Wakilan Majalisar sunyi ta aikawa juna naushi, alamarin da yasa wasunsu tserewa daga bakin aikin nasu.Duk da wannan hali da Majalisar ta tsinci kanta ayau, Wakilan sun sami amincewa da yarjejeniyar, da zata amince kasar Russia ta kafa sansanin ta agaban ruwan kasar ta Ukraine na tsawon shekaru 50.Ita kuma kasar Russia zata saidawa kasar Ukraine iskar Gas da take bukata cikin rahusa da ragin zai kai kashi 30%, ragi da ake ganin zai sa kasar Ukraine tayi tsimin kudin daya kai Dollan Amirka Billion 40.Wakilan Majalisar kasar dai ta amince da wannan yarjejeniya tsakanin kasashen biyu.Prime Ministan Kasar Russia Vladimir Putin ajiya yana kasar Ukraine domin kara kulla wannan yarjejeniya tsakanin kasashen biyu. 

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.