Isa ga babban shafi
Thailand

An Cigaba Da Bore Yau

Bisa dukkan alamu dai yarjejeniyar sulhu, tsakanin Gwamnatin kasar Thailand da masu bore cikin jajjayen kaya, da sukayi churko- churko awasu muhimman wurare abirnin Bangkok, taci tura.   A dazunnan masu boren sukace zasu cigaba da boren, saboda Gwamnatin kasar ta gaza biya masu bukatun nasu da suka gabatarwa Gwamnatin kasar. 

Les chemises rouges menacent les forces de police près de l'hôtel SC Park, à Bangkok, le 16 avril 2010.
Les chemises rouges menacent les forces de police près de l'hôtel SC Park, à Bangkok, le 16 avril 2010. rfi
Talla

An zaci Gwamnatin kasar zata bada kai ayau, to amma Prime Minitan  kasar Abisit Vajjajiva yace allambaran, bukatar masu boren dake neman ya rusa majalisar kasar ayi zabe cikin kwanaki 30, ba zata sabu ba.

Masu boren wadanda suke sanye da jajjayen kaya, magoya bayan Tsohon Premiyan kasar ne Thaksin Shinawatra.

Sun fadi cewa zasu kawo karshen boren da sukeyi da mamaye wurare a birnin Bangkok da zaran Gwamnatin kasar ta rusa  majalisar kasar da tsaida ranar zabe cikin kwanaki 30.

Bayanai na nuna cewa Prime Ministan Kasar yayi wani taro ayau da Kusoshin Gwamnatin kasar, inda ake zaton zasu bada kai, saidai kuma an kare taron ba tare da kawo karshen wannan bore ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.