Isa ga babban shafi
Thailand

Sojan Sunyi Barazanar Fito Na Fito

A kasar Thailand Soja sun gargadi masu boren gama gari dasu shiga taitayinsu, su daina, gudun kada asami hasarar rayuka. Sojan zsun nuna cewa ashirye suke domin yin fito na fito da masu boren nuna kyamar Gwamnatin kasar, wadanda ke cikin jajayen riguna, atsakiyar birnin Bangkok.Babu abinda sojan da sauran jamian tsaro basuyi ba domin fasa taron masu bore amma ya faskara.Akalla mutane 25 ne suka mutu alokacinda boren ya munana afarkon wannan watan.Ayarin masu boren wadanda suke cikin jajayen riguna na neman Gwamnatin kasar ta sauka ne, da neman ayi sabon zabe.Mai Magana da yawun Sojan kasar Sunsern Kaewkumnerd, ya fadi cewa lokaci yayi da masu bore zasu daina ko kuma asa kafar wando daya dasu. 

Les forces de sécurité thaïlandaises le samedi avril 2010.
Les forces de sécurité thaïlandaises le samedi avril 2010. Reuters/Sukree Sukplang
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.