Isa ga babban shafi
Bangkok

Bam Ya tarwatse A Bangkok

Bama bamai, har biyar ayau sukayi ta tarwatsewa a birnin Bangkok na kasar Thailand inda mutane keta yin bore na tsawon kwanaki masu yawa. Bayanai da dimi dimi na nuna mutane akalla 50 ne suka sami munanan raunuka, awani alamari da ake ganin boren ya kazanta sosai.Dakarun kasar dazun nan, dauke da manyan makamai ne dai suka yi ta kutsawa yankin da masu boren sukayi dandazo domin hana boren.Kanar Sansern Kaewkamnerd ya fadawa kamfanin Dillancin labaran Reuters cewa bama baman da suka tarwatse na gaske ne kirar wadanda ake saba su a kafada da sukayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 25 a lokacin boren da aka fara watan jiya.Mutane akalla 500 ne dai suke harabar da bama baman sukayi ta tashi.Tunda fari Sojan kasar suka yi barazanar cewa zasu tunkari masu bore gaba da gaba. 

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.