Isa ga babban shafi

'Yan Indonesia miliyan 123 za su koma gida domin bukukuwan Sallah karama

'Yan kasar Indonesia miliyan 123 ne ake saran zasu bar inda suke daga gobe alhamis domin komawa garuruwan da suka fito dan gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr, wanda aka saba yi bayan kammala azumin watan Ramadana. 

Wsu  'yan kasar Indonesia yayin kokarin komawa gida daga sassan duniya don gudanar da bikin Salla Idi karama.
Wsu 'yan kasar Indonesia yayin kokarin komawa gida daga sassan duniya don gudanar da bikin Salla Idi karama. © JUNI KRISWANTO / AFP
Talla

Wadannan mutane miliyan 123 za suyi amfani da babura da kananan motoci da safa-safa da jiragen sama da kuma kwale kwale wajen tafiya garuruwan su domin shiga bikin sallar daga gobe alhamis. 

Yanzu haka tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin mota sun fara cika da matafiyan, yayin da filayen jiragen sama da na motocin safa safa suma suka samu karuwar matafiyar dake kokarin komawa domin saduwa da ‘yan uwa da abokan arziki. 

Wannan shine karo na farko da za’a samu irin wadanan tafiye tafiye tun bayan barkewar annobar korona wadda ta hana zirga zirga a kasar da tafi yawan al’ummar Musulmi a duniya. 

Ma’aikatar sufurin kasar tayi hasashen cewar mutane miliyan 123 ake saran su koma garuruwansu domin gudanar da bukukuwan sallar, wanda ya nuna na samu kari daga miliyan 85 da aka gani bara a irin wannan lokaci. 

Daga cikin wadannan matafiya akalla miliyan 18 ake saran su bar yankin Greater Jakarta kawai, inda zasu fuskanci kuncin yawan ababan hawa hanya. 

Hukumomin kasar sun rufe wasu hanyoyin domin baiwa matafiya damar barin biranen ba tare da samun kunci ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.