Isa ga babban shafi

Dan bindiga ya kashe kananan yara 36 a Thailand bayan bude wuta a makaranta

Akalla kananan yara 36 suka mutu bayan da wani tsohon dan sandan Thailand ya kai hari wata makarantar yara dauke da bindiga da kuma wuka, gabanin ya kashe kansa da iyalinsa bayan tafka aika-aikar.

Yankin da dan bindiga ya kai hari a Thailand.
Yankin da dan bindiga ya kai hari a Thailand. © AP
Talla

Rahotanni sun ce da misalin karfe 12 da rabi na rana agogon kasar ne, maharin ya afkawa makarantar wadda ke lardin Nong Bua Lam Phu tare da bude wuta kan mai uwa da wabi gabanin tserewa, inda daga bisani kuma ya isa gida ya kashe kansa da matarshi da kuma dansa.  

Kakakin Firaministan kasar, Anucha Burapachaisri ya ce yaran da suka mutu a harin ya haura 30 baya ga ma’aikatan makarantar da dama.

Wani jami’in dan sanda daga yankin da abin ya faru, ya bayyana maharin da suna Panya Khamrab mai shekaru 34 wanda aka kora daga aiki bara saboda ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Wata ganau da ta ci kari da Panya lokacin da ya ke kokarin tserewa daga wajen da ya kai harin, da aka bayyana sunanta da Paweena Purichan ta ce da idonta taga maharin ya na tuka babbar mota akan titi inda ya ke kokarin nike wasu kananun motoci da ke gabansa ko da ya ke sai da ya kade wasu mutum biyu da ke tafiya akan mashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.