Isa ga babban shafi

Taliban ta rufe makarantun mata sa'o'i bayan bude su

Kungiyar Taliban ta bukaci rufe makarantun dalibai mata yau Laraba, sa’o’i bayan bude su da aka yi domin fara karatu, matakin da ya jefa su cikin damuwa da kuma rudani akan manufofin kungiyar.

Dalibai mata a wata makaranta da ke Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.
Dalibai mata a wata makaranta da ke Kabul, babban birnin kasar Afghanistan. AP - Rahmat Gul
Talla

Sauya matsayin Taliban dangane da bude makarantun bayan dubban dalibai mata sun koma azuzuwa a karon farko tun watan Agustan bara da suka kwace iko, ya haifar da fargaba dangane da makomar karatun ‘yammata a kasar.

Ma’aikatar ilimi bata ce uffan ba dangane da sabon matakin, yayin da shugabannin ta suka gudanar da bukukuwan sake bude sabon zangon karatun a birnin Kabul.

Dalibai mata a kasar Afghanistan, yayin daukar karatu a makarantarsu da ke birnin Herat.
Dalibai mata a kasar Afghanistan, yayin daukar karatu a makarantarsu da ke birnin Herat. AP - Petros Giannakouris

Kakakin ma’aikatar ilimi Aziz Ahmad Rayan ya ce akwai sarkakiya dangane da fara karatun mata a kasar, yayin da ya bayyana cewar mai magana da yawun kungiyar Taliban zai yi karin haske akai nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar daukar matakin rufe makarantun matan ya biyo bayan taron da manyan jami’an Taliban suka gudanar a birnin Kandahar wanda yake cibiyar mayakan.

Wata malama a makarantar mata ta Omara Khan da ake kira Palwasha ta ce ta ga wasu daga cikin daliban suna zub da hawaye saboda rufe makarantun.

Shugabar hukumar kare hakkin Bil Adam ta majalisar Dinkin Duniya kuwa, Michelle Bachellet ta bayyana matukar damuwa dangane da matakin, wanda tace ya sabawa kudirorin majalisar na baiwa mata da ‘yan mata ilimi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.