Isa ga babban shafi
Taliban-Mata

Taliban ta tarwatsa dandazon Mata da ke zanga-zangar neman 'yanci

Rahotanni daga birnin Kabul na Afghanistan sun ce jami’an tsaron Taliban sun yi amfani da hayaki mai sanya kwalla kan dandazon matan da suka fita zanga-zangar kalubalantar matakin hana su aiki da karatu.

Matan da suka gudanar da zanga-zangar kalubalntar rashin basu damar karatu da aiki a Afghanistan.
Matan da suka gudanar da zanga-zangar kalubalntar rashin basu damar karatu da aiki a Afghanistan. Wakil Kohsar AFP
Talla

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP da ya zanta da wasu mata 3 da ke cikin masu boren na jiya lahadi, sun bayyana yadda suka gaji da dokokin na Taliban tun bayan karbar ragamar kasar a watan Agustan 2021.

AFP ya ruwaito yadda mata akalla 20 suka taru a kofar jami’ar Kabul rike da kwalaye masu rubutun ‘‘tabbatar da adalci da tabbatar da daidaito’’ a bangare guda kuma wasu ke dauke da rubutun ‘‘yancin Mata ‘yancin dan adam’’

Sai dai sa’o’I kalilan da fara boren jami’an tsaron Taliban suka tarwatsa masu boren ta hanyar yi musu feshin hayaki mai sanya hawaye.

Tun bayan hawan Taliban mulkin Afghanistan, kungiyar ta gindaya dokoki da suka ci karo da manufofin kasashen Duniya ciki har da hana Mata damar karatu da aiki.

Haka zalika karkashin mulkin na Taliban babban laifi ne gudanar da zanga-zanga matakin da acewar rahotanni hakan ya hana mutane fita yin bore don kalubalntar halin da kasar ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.