Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta rushe hukumar zaben kasar Afghanistan

Kungiyar Taliban ta rusa hukumar zaben kasar Afganistan, wadda ta shirya tare da sa ido kan zabukan da suka gudana a zamanin gwamnatin da ta gabata, wadda kasashen yammacin Turai ke marawa baya.

Ministan harkokin wajen Afghanistan a karkashin gwamnatin Taliban.
Ministan harkokin wajen Afghanistan a karkashin gwamnatin Taliban. AP - Muhammad Farooq
Talla

Yayin sanar da matakin a jiya Asabar, kakakin gwamnatin Taliban Bilal Karimi ya ce, a halin yanzu babu bukatar ci gaba da wanzuwar hukumar zaben Afghanistan tare da wasu makamantanta, wato hukumar da ke karbar korafe korafen zabe mai zaman kanta ta kasar.

A watan Agustan da ya gabata kungiyar Taliban ta sake mamaye madafun ikon kasar a daidai lokacin da Amurka ta fara janye dakarunta da suka shafe shekaru 20 sun yaki da Taliban da kuma ‘yan ta’adda na kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.