Isa ga babban shafi
Taliban-MDD

Gwamnatin Taliban ta yiwa mutane fiye da 100 kisan gilla- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da karbar korafe-korafe kan zargin kisan gilla har fiye da 100 daga al’ummar Afghanistan tun daga lokacin da Taliban ta kwace iko da mulkin kasar zuwa yanzu.

Wasu mayakan Taliban.
Wasu mayakan Taliban. © Credit: ASSOCIATED PRESS
Talla

Mataimakiyar shugabar hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniyar Nada Al-Nashif ta ce karuwar bayanan kisan gillan daga gwamnatin taliban abin damuwa ne matuka.

A wani zaman mambobin hukumar a Geneva, Al-Nashif ta ce sun samu kwararan bayanai kan yadda Taliban ta yiwa mutane fiye da 100 kisan gilla tsakanin watan Agusta zuwan Nuwamban daya gabata, galibinsu tsaffin jami’an gwamnatin kasar da suka taka rawa wajen yaki da ayyukan kungiyar a baya.

Babbar jami’ar ta ce mutane 72 daga cikin fiye da 100 da aka yiwa kisan gillar, Taliban ce da kanta ta yi su, yayinda wani kaso na adadin kuma mabanbantan mutane suka aiwatar ko dai da nufin daukar fansa ko kuma wani abu makamancin haka.

Bayanan hukumar ya nuna cewa, Taliban ta aiwatar da kashe-kashen ne a bainar jama’a ba tare da wata fargabar boyewa ba.

Kalaman na hukumar kare hakkin dan Adam na zuwa ne bayan tun farko Amurka ta yi makamancin zargin na cewa Taliban ta take hakkin dan adam ta hanyar kisan gill aga daruruwan tsoffin jami’an tsaron gwamnatin Afghanistan da suka mika wuya gareta bayan kwace ikonta.

Hukumar ta ce cikin wadanda Taliban ta yiwa kisan gillar, har da mambobin hukumar leken asiri ta kasar da dakarun Soji dana ‘yan sanda da kuma jami’an fikira.

Sai dai tuni kakakin gwamnatin ta Taliban Qari Sayed Khosti ya musanta zarge-zargen yana mai cewa babu gaskiya a cikin bayanan da hukumar ta bayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.