Isa ga babban shafi
Afghanistan

Amurka ta yi tir da Taliban kan kisan tsoffin jami'an Afghanistan a boye

Amurka ta jagoranci wasu gungun kasashen yammacin Turai da wasu kawayenta wajen yin Allah wadai da Taliban kan kisan gillar da kungiyar ta yi wa wasu tsoffin jami'an tsaron Afganistan, ta’asar da kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suka bankado, inda suka bukaci a gudanar da bincike cikin gaggawa.

Wasu mayakan kungiyar Taliban a Afghanistan.
Wasu mayakan kungiyar Taliban a Afghanistan. Ahmad SAHEL ARMAN AFP
Talla

A farkon makon da ya kare kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto da ta ce ta tattara bayanan kashe wasu tsaffin jami'an tsaron Afghanistan 47 da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma jami'an leken asiri, wadanda suka mika wuya ga mayakan Taliban ko kuma aka kama su daga tsakiyar watan Agusta zuwa Oktoba.

A cikin watan Agustan da ya gabata kungiyar Taliban ta sake kwace iko da mulkin kasar Afghanistan bayan shafe shekaru 20 da fatattakarsu da sojojin Amurka suka yi.

Wasu mayakan Taliban bayan kwace iko da fadar gwamnatin Afghanistan a birnin Kabul, ranar 15 ga watan Agustan, 2021.
Wasu mayakan Taliban bayan kwace iko da fadar gwamnatin Afghanistan a birnin Kabul, ranar 15 ga watan Agustan, 2021. © ASSOCIATED PRESS

Bayan sake kafuwarsu ne kuma, shugabannin Taliban dake neman karbuwa daga kasashen duniya suka yi alkawarin sauya tsarin mulkin da aka san kungiyar da shi a shekarun baya.

Cikin rahotonta, kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce shugabannin na Taliban sun ba da umarnin ga tsoffin jami'an tsaron da suka mika wuya, da su yi rajista da hukumomi domin a tantance su, da kuma karbar wasikar dake tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Sai dai 'yan Taliban din na amfani da tantancewar wajen tsarewa da aiwatar da kisan gilla, ko kuma batar da mutanen cikin ‘yan kwanaki bayan sun yi rajistar da aka bukaci su yi, inda suke yasar da gawarwakinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.