Isa ga babban shafi
Amurka - Afghanistan

Rayukan 'yan jaridun Afghanistan na cikin hatsari saboda Taliban - RSF

Kungiyar 'Yan Jaridu ta kasa da kasa RSF, ta bukaci Shugaban Amurka Joe Biden ya tsara shiri na musamman domin kwashe' yan jaridar Afghanistan da ke cikin hatsari daga birnin Kabul da ke karkashin ikon Taliban.

'Yan jaridar Afganistan yayin wani rahoto na labarai game da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Taliban da Amurka, a Shahr-e-Naw. Park a Kabul. 30 Afrilu 2019.
'Yan jaridar Afganistan yayin wani rahoto na labarai game da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Taliban da Amurka, a Shahr-e-Naw. Park a Kabul. 30 Afrilu 2019. © Wakil Kohsar/AFP/Getty Images
Talla

RSF ta ce a halin yanzu Amurka ta damu ne kawai da kwashe ‘yan kasarta da tsoffin ma'aikata daga Afghanistan.

Kungiyar ‘Yan Jaridun ta Duniya ta ce yanzu haka ta samu daruruwan takardun bukatar taimako daga ‘yan jaridar Afganistan, galibinsu mata, wadanda ke cikin firgici da fargaba.

Cikin makon da ya kare yayin neman dan jaridar Deutsche Welle da yanzu haka ke zaune a Jamus, mayakan kungiyar Taliban suka harbe wani dan uwan dan jaridar tare da raunata wani, a ranar Laraba kamar yadda gidan rediyon Jamus din ya ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.