Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta amince da kasafin kudinta na farko

Kungiyar Taliban ta amince da kasafin kudinta na farko domin tafiyar da ayyukan gwamnatin ta a Afghanistan tun bayan da masu tsatsauran ra'ayin suka koma kan karagar mulki a cikin watan Agusta.

Mukaddashin miniatan harkokin wajen kasar Afghanistan Amir Khan Muttaqi.
Mukaddashin miniatan harkokin wajen kasar Afghanistan Amir Khan Muttaqi. AP - Burhan Ozbilici
Talla

Shugabannin na Taliban sun sanar da kasafin na su ne ba tare da ambaton taimakon kasashen waje ba, wanda ta ce yawan kasafin ya kai, dalar Amurka miliyan 508.

Taimakon kasa da kasa da Afghanistan ke samu a lokacin da Amurka ke marawa tsohuwar gwamnatin kasar baya, ya kai kashi 80 cikin 100 na kasafin kudinta.

Kakakin ma'aikatar kudin gwamnatin kungiyar Taliban Ahmad Wali Haqmal, ya ce a karon farko cikin shekaru 20, sun yi kasafin kudin da bai dogara da taimakon kasashen waje ba, abinda ya bayyana a matsayin babbar nasara ga kasar.

Haqmal ya ce ma’aikatan kasar, wadanda da yawa daga cikinsu ba a biya su albashi ba, za su fara karbar albashi a karshen watan Janairu, kuma haka abun yake ga mata, wandanda akasari aka hana su zuwa aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.