Isa ga babban shafi
Taliban-Mata

Taliban ta haramtawa Mata bulaguro ba tare da muharrami ba

Taliban da ke jagorancin Afghanistan ta haramtawa mata tafiye tafiye ba tare da muharrami ba, cikin wani sabon tsari da ta fitar yau lahadi a wani yunkuri na dakile yawaitar tafiye-tafiyen mata su kadai karkashin jagorancin kungiyar da ke ikirarin addini.

Rayuwar Mata ta fada halin tsaka mai wuya karkashin ikon Taliban.
Rayuwar Mata ta fada halin tsaka mai wuya karkashin ikon Taliban. Hector RETAMAL AFP
Talla

Sanarwar da gwamnatin ta Taliban ta fitar ta ce za a sahalewa mata iya yin gajeran balaguro ne kadai ba tare da muharrami ba kwatankwacin tafiyar kilomita 72.

Karkashin sabbin tsare-tsaren ya kuma sahalewa mata masu motar kansu su iya tuka kansu don yin zirga-zirga a cikin gari amma dole sai suna sanye da cikakken hijabin musulunci.

Kakakin ma’aikatar al’amuran addaini Sadeq Akif Muhajir ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa dole ne duk macen da za ta yi balaguro daga yau lahadi matukar za ta yi tafiyar da ta haura mil 45 sai tana tare da wani namiji daga ahalinta.

Wannan mataki dai na zuwa ne makwanni kalilan bayan Taliban ta umarci gidajen talabijin na kasar su daina haska wasanni dirama ko kuma tallace tallacen da ke dauke da mata a ciki.

Haka zalika karkashin dokokin Taliban wajibi ne matan da ke aiki a gidajen talabijin su sanya cikakken hijabi lokacin da suke gabatar da shirye-shiryensu ba tare da nuna fuskarsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.