Isa ga babban shafi
Asiya-Amurka

Zanga-zangar adawa da zuwan Donald Trump a Taron Asiya

Yan Sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa daruruwan mutanen da suka shiga zanga zangar adawa da sughaban Amurka Donald trump a wajen taron shugabanin kasashen Asia da ake gudanarwa a Manila.

Masu zanga-zangar adawa da zuwa Donald Trump a Asiya
Masu zanga-zangar adawa da zuwa Donald Trump a Asiya REUTERS/Kim Hong-Ji
Talla

Masu zanga zangar sun yi mutum mutumin Trump mai dauke da hannaye 4 da sukayi tattaki da shi, da kuma rubutun dake cewa ‘Trump ka koma gida’ da kuma ‘A haramtawa Trump, dan ta’adda na farko’.

Yan Sanda sun ce masu zanga zangar sun kai kusan 2,000, yayin da aka jikata jami’an su guda 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.