Isa ga babban shafi
Syria

An kwashe fararen hula dubu 25 a Aleppo

Kungiyar bayar da agajin gaggawa ta kasa da kasa Red Cross ta bayyana cewa, akalla mutane dubu 25 ne suka fice daga birnin Alepo na Syria tun bayan da aka fara kwashe fararen hula a makon jiya. 

An kwashe fararen hula 25 daga gabashin birnin Aleppo na Syria
An kwashe fararen hula 25 daga gabashin birnin Aleppo na Syria REUTERS/Abdalrhman Ismail/File Photo
Talla

Mai magana da yawun kungiyar Ingy Sedky ta ce, a jiya Litinin kadai, sun kwashe mutane dubu 15 a gabashin birnin na Aleppo .

Jami’ar ta kara da cewa, a halin yanzu, dubban jama’a na ci gaba da dakon kwashe su a motocin safa.

Tun bayan da aka cimma yarjejeniyar kwashewar, kungiyar bada agajin ke sanya ido kan yarjejeniyar wadda Rasha da Turkiya suka amince da ita.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.