Isa ga babban shafi
Syria

Syria: Dakarun Assad sun kwace ikon gabashin Aleppo

Dakarun gwamnatin Bashar Al Assad na Syria sun kwace ikon gundumar Sakhour daga hannun ‘Yan tawaye, da ke yankin gabashin Aleppo, a yayin da dakarun ke ci gaba da kutsawa domin kakkabe ‘yan tawayen daga garin baki daya.

Dakarun gwamnatin Syria na ci gaba da kutsawa domin kwato Aleppo daga hannun 'Yan tawaye
Dakarun gwamnatin Syria na ci gaba da kutsawa domin kwato Aleppo daga hannun 'Yan tawaye REUTERS/Abdalrhman Ismail/File Photo
Talla

Dubban fararen hula ne suka fice daga yankin bayan shafe lokaci ana barin wuta tsakanin dakarun da ‘Yan tawaye a yankin na gabashin Aleppo.

Kungiyar da ke sa ido a rikicin Syria ta ce dakarun gwamnatin sun kwace ikon gundumomin Sakhour da Haydariya da Shaeikh Khodr.

Gwamnatin Rasha da ke taimakawa dakarun Syria ta ce gundumomi 12 ne dakarun gwamnatin suka kwace a gabashin Aleppo.

Kwace ikon gundumomin dai babbar baraka ce ga ‘Yan tawayen da suka kwace ikon Aleppo tun a 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.