Isa ga babban shafi
Syria

Sojan Kasar Syriya na ci gaba da samun nasara a Aleppo

Fararen hula na ci gaba da tserewa daga birnin Aleppo a yayin da dakarun gwamnatin  ke ci gaba da kara karbe wasu unguwanni daga hannun 'yan tawayen.  

Wani gefe na birnin Aleppo a kasar Sirya
Wani gefe na birnin Aleppo a kasar Sirya Mahmoud Hebbo/Reuters
Talla

Wannan dai ba karamin koma baya ba ne ga 'yan tawayen da ke rike da yankin gabashin birnin tun cikin shekarar 2012.

Rahotanni daga birnin na cewa daruruwan mutane ne ke ci gaba da ficewa daga bangaren 'yan tawaye suna komawa yankin dake karkashin ikon gwamnati tun bayan da dakarunta suka karbe wata babbar unguwa daga 'yan tawayen.

Sake kwace unguwar ta Massaken Hanano da dakarun gwamnatin suka yi a ranar Assabar abin farin ciki ne ga bangaren shugaba Bashar Al’assad da dakarunsa wadanda tun ranar 15 ga watan Nuwamba  suka kaddamar da harin a kokarinsu na ganin ta ko halin kaka sun sake karbe yankin gabashin na Aleppo da ya kubuce masu tun cikin 2012 da kuma ta killace yau da watanni 4 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.