Jiragen yakin Syria sun kai hare-hare sama da 150 cikin awwani 24
Mazauna birnin Aleppo sun ce jiragen yakin Syria sun kaddamar da sabbin hare-hare sama da 150 cikin awanni ashirin da hudu da suka gabata, hakan kuma yayi sanadin rasa rayukan sama da mutane 90 a arewacin birinin.
Wallafawa ranar:
Hare-haren da aka kaddamar a yau Juma’a, bangare ne na sabon yunkurin da gwamnatin Syria ta kaddamar, domin kwace yankunan da ke karkashin ikon ‘yan tawaye a birnin Aleppo.
Harin yayi sanadin lalata kayayyakin bada agajin gaggawa da ke yankin tare da lalata wuraren karkashin kasa da fararen hula suke amfani da su wajen fakewa hare-haren bam.
Rahotanni sun ce, cigaba da luguden wutar a birnin Aleppo yana dakile kokarin jami’an bada agaji, na ceto fararen hula da sabon fadan ya ritsa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu