Isa ga babban shafi
Syria

An kai harin makami mai guba a Aleppo

Wani Rahotan bincike da jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka gudanar ya zargi gwamnatin Syria da harba makami mai guba na Chlorine kan wani yanki na Aleppo, abinda ya yi illa ga mutane 80.

Ana zargin gwamnatin Syria da amfani da makami mai guba a yankin Aleppo
Ana zargin gwamnatin Syria da amfani da makami mai guba a yankin Aleppo GEORGE OURFALIAN / AFP
Talla

Ma’aikatan kai daukin gaggawa sun bayyana cewa, a halin yanzu, mutane na fama da matsalar numfashi sakamakon harin wanda aka kai a Sukari da ke gabashin Aleppo.

Sai dai gwamnatin ta Syria ta sha musanta amfani da makami mai guba wajen kai hare-hare.

Wannan dai na zuwa ne a dai lokacin da ‘yan adawar kasar ke shirin ganawa a birnin London don tattaunawa kan shirin kawo karshen rikicin shekaru biyar da ya lakuma rayuka da dama tare da tilasta wa miliyoyi kaurace wa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.