Rasha ta amince ta dakatar da kai hari Aleppo
Kasar Rasha ta ce a shirye ta ke, ta dakatar da luguden wuta kan ‘yan tawaye a Aleppo na Syria har na tsawon sa’o’i Arba’in da takwas kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukata.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Rashan Igor Konashenkov ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce Rasha ta yanke shawarar saboda ba masu kai kayan agaji damar isa ga fararen hula da fada ya ritsa da su a Aleppo.
Sai dai Rasha ta ce tana jiran bayani daga Majalisar Dinkin Duniya kan kammala shirin jami’an kai agajin, kafin daga bisani a sanar da ranaku da kuma lokutan da tsagaita wutar zata fara aiki.
A cewar ma’aikatar tsaron Rasha za a tabbatar da tsaron jami’an Majalisar Dinkin Duniyar yayin gudanar da ayyukansu na agaji.
Satin da ya gabata ne kasar Rasha ta yi tayin tsagaita wuta na tsawon sa’o’i uku a Aleppo tayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ki amincewa da shi, a cewarta lokacin ba zai isa a kai agaji ga sama da mutane miliyan daya da rabi ba da ke matukar bugatar agaji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu