Isa ga babban shafi
Syria-Amurka-Rasha

Rasha ta musanta karya dokar Majalisar dinkin Duniya

Kasar Rasha ta ce amfani da ta yi da filin jirgin kasar Iran wajen tashin jiragen yakinta don kai hari kan mayakan IS a Syria bai sabawa dokar Majalisar dinkin Duniya ba, wadda ta hana amfani da filin jiragen saman Iran domin wannan manufa.  

Jigin yakin kasar Rasha
Jigin yakin kasar Rasha Reuters/路透社
Talla

Ministan harkokin waje na Rashan Sergei Lavrov ne ya bayyana haka bayan gwamnatin Amurka ta yi zargin cewa Rasha na’iya sabawa dokar kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniyar sashi na 2231, ta hanyar amfani da Iran wajen kai hari a Syria.

Sashin dokar dai ya haramta cinikayyar makamai ko taimakawa Iran din da karfin soji ba tare da amincewar Majalisar dinkin Duniya ba.

Kasar Amurka ta sha zargin Rasha cewa harin da take ikirarin kaiwa kan mayakan IS tana maida hankali ne kan ‘yan tawayen Syria masu samun goyon bayanta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.