Isa ga babban shafi
Syria

O'Brien ya bayyana takaicinsa kan rikicin Aleppo

Babban Jami’an jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Stephen O’Brien ya bayyana bacin ransa kan yadda manyan kasahsen duniya suka kasa cimma matsaya kan tsagaita wuta a Aleppo da ke kasar Syria domin kai kayan agaji ga mabukata.

Babban Jami'in Jin kai na MDD Stephen O'Brien
Babban Jami'in Jin kai na MDD Stephen O'Brien AFP PHOTO / KHALIL MAZRAAWI
Talla

Stephen O'Brien ya gaya wa kwamitin sulhu cewa sun yi tanadin da ya dace na tura manyan motocin kayan agaji zuwa gabashin Aleppo amma idan bangarorin kwamitin sun amince da yarjejeniyar tagaita wuta a tsakaninsu.

Mista O’Brien ya bayyana takaicin shi akan yadda aka kasa samun matsaya a kwamitin sulhu a zaman taron da suka gudanar karo na uku akan halin da yankin Aleppo ke ciki.

Tun a watan Yuli ne dakarun gwamnatin Bashar al Assad suka kewaye gabashin Aleppo da ‘yan tawaye ke iko, al’amarin da ya jefa mutane sama da dubu dari biyu da hamsim cikin mawuyacin hali na katsewar abinci da ruwan sha da magunguna da hasken lantarki.

Jami’in ya sake yin kira ga bukatar tsagaita wuta a Aleppo na tsawon sa’oi 48 domin samun isar da kayan jin-kai ga dimbin jama’ar da dakarun gwamnatin Syria suka yi wa kawanya.

O’Brien ya yi kira ga Amurka da Rasha da su aje sabanin da ke tsakaninsu akan rikicin Syria domin ganin an tsagaita wuta.

Wannan korafi na shi na zuwa ne kwana guda bayan mummunan sukar da shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ya yi wa Majalisar cewar ba ta da amfani domin ta kasa magance tashe-tashen hankulan da ake samu a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.