Isa ga babban shafi
Syria

Rikici ya barke a kokarin kwato birnin Aleppo

Kasashen Amurka da Rasha sun yi musayar kalamai masu zafi dangane da rawar da kowanne bangare ke takawa a fafatawar da ake wajen mallakar Aleppo dake kasar Syria.

Birnin Aleppo, cibiyar tattalin arzikin Syria
Birnin Aleppo, cibiyar tattalin arzikin Syria REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Bayani na nuna cewar ana ci gaba da musayar wuta tsakanin Yan adawar Syria dake samun goyan bayan Amurka da kawayen ta da sojojin gwamnatin Syria mai samun goyan bayan Russia dan mallakar garin Aleppo, cibiyar tattalin arzikin kasar.

Yan adawar sun kaddamar da wani sabon harin karbe ikon daukacin birnin ranar lahadi, wanda ake ganin zai basu damar samun gagarumar nasara a yakin da ake gwabzawa a kasar.

A bangare daya gwamnatin Syria na ci gaba da kai hari dan rike akasarin Yankunan birnin dake hannun ta, yayin da jiragen saman Russia ke kai nasu hare haren.

Jakadiyar Amurka a kwamitin Sulhu Samanther Power ta zargi Russia da haifar da tarnaki wajen kai kayan agaji ga dubban mutanen dake birnin, yayin da Russia ta zargi Amurka da munafucin cikin yakin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.