Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan tawaye sun kori dakarun Syria a Aleppo

Gwamnatin Syria ta sake tura dakarunta zuwa yankin Aleppo bayan ‘Yan tawaye sun sanar da karya lagon dakarun a yankin da suka yi wa kawanya. Dakarun na Syria dai na tsoron mamaya ne daga ‘Yan tawayen a yankin da suke iko a Aleppo.

Mutanen yankin Aleppo na murna kan nasarar da 'Yan tawaye suka samu akan dakarun Syria
Mutanen yankin Aleppo na murna kan nasarar da 'Yan tawaye suka samu akan dakarun Syria REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce ‘Yan tawayen sun kori dakarun na Gwamnatin Bashar al Assad daga yankin na Aleppo, domin bude hanya ga mutanen yankin na gabashi masu makwabtaka da Aleppo da aka mamaye.

Yanzu dai murna ta barke tsakanin mutanen yankin sama da dubu dari da ashirin da biyar da ke bukatar agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.