Isa ga babban shafi
Thailand

Zaben raba gardama a Thailand

Al'ummar kasar Thailand, na kada kuri’u a zaben raba gardamar amincewa da sabon kudin tsarin mulkin kasa, da ‘yan adawa ke gargadi cewa, ba shi da maraba da salon mulkin soji da kuma haifar da rabuwar kawunan.

Zaben raba gardama a Thailand
Zaben raba gardama a Thailand REUTERS/Chaiwat Subprasom
Talla

Zaben na wannan lokaci na baiwa al’ummar kasar daman kada kuri’u a karon farko tun bayan hambarar da gwamantin Yingluck Shinawatra a shekarar 2014.

A cewar sojin kasar, sabon kudin tsarin mulkin kasar zai shawo kan rikicin Siyasa da kawo daidaito a kasar da lamura ke sake rincabewa.

A na cigaba da sokar gwamnatin sojin kasar kan tauye haki dan adam da amfani da karfi wajen aiwatar da dokoki da zai durkusar da demokradiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.