Isa ga babban shafi
Saudi- Philippine

Wakilan Philippine za su Saudiyya don taimakawa 'yan kasar da suka makale

Kasar Philippine ta ce za ta tura jami'an ta zuwa Saudiyya nan da lokaci kadan, don taimakawa dubban ‘yan kasar ta Philippines da suka makale bayan sallaman su daga  wuraren ayyukan da suke yi.

Shugaba Rodrigo Duterte na kasar Philippine
Shugaba Rodrigo Duterte na kasar Philippine REUTERS/Erik De Castro
Talla

Gwamnatin Philippines ta ce ayarin jami'an ta na farko za su tafi Saudiyya Laraba mai zuwa, don bada taimako da ya dace ga ‘yan Philippines dake tsugune a wasu sansanoni.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama a kasar Philippines na cewa dimbin ‘yan kasar sun makale a Saudiyya wasu na bara don samun abinci, wasu kuma na cikin wani hali saboda gaza samun albashi na tsawon wani lokaci, bayan sun rasa ayyukansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.