Isa ga babban shafi
AFGHANISTAN

kungiyar Taliban ta nada sabon shugaba

Kungiyar Taliban a kasar Afghanistan ta sanar da nadin Mawlawi Haibatullah Akhundzada a matsayin sabon shugabanta bayan  tabbatar da mutuwar Mullah Akhtar Mansour shugaban kungiyar sakamakon harin da jiragen yakin Amurka da babu matuki sukayi dan tsakanin nan.

Mayakan kungiyar Taliban
Mayakan kungiyar Taliban AFP PHOTO / Noorullah Shirzada
Talla

Mawlawi Haibatullah Akhundzada, dai malami ne da ya jagoranci bangaren shari’ar kungiyar  a baya kuma yana daya daga cikin manyan shugabanin kungiyar kafin nada shi yau a matsayin sabon shugaban kungiyar ta Taliban da ya maye gurbin Mullah Akhtar.

Hakazalika sanarwa da kungiyar ta bayar na cewa an nada wasu mutum 2 dasu zama sabbin mataimakan sabon shugaban wato Sirajuddin Haqqani da Mullah Yakubu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.